Pages

Saturday 15 June 2019

Buhari be kula gwamnoni ba akan nadin ministoci

Rahotanni sun bayyana cewa ba kamara a bayana, a wannan karin gwamnoni basu da damar yin ruwa da tsaki akan nada ministoci. Shugaban kasa, Muhammadu Buhari be basu wannan damar ba.




Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, suma gwamnonin a wanna karin sun zama 'yan kallo masu jiran tsammani kamar sauran 'yan Najeriya akan su wanene zasu zama ministocin shugaban kasar a zangon mulkinshi na 2.

Wani gwamna da ba'a bayyana sunanshi ba ya gayawa jaridar cewa, har zuwa yanzu shugaban kasa, Buhari be bukaci gwamnoni su aike mai da sunayen wanda za'a baiwa ministoci ba.

Yace sun dai mika sunayen wanda suke so a baiwa amma be ce musu Eh ko A'a ba.

Hakanan rahoton yace ministocin da suka yi aiki a zangon mulkin Buharin na farko ma babu wanda ke da tabbacin za'a sake nadashi mukamin, saidai sun tare a Abuja suna ta bikon sake samun mukaman.

Rahoton Vanguard kuwa cewa yayi mutane 3 ne suke ruwa da tsaki akan wanda za'a nada ministocin. Mutanen kuwa sune Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da kuma shugaba jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole.

Saidai duk wadannan mutanen 3 ba wai tare suke aiki ba, kowa na kokarin ganin ya kawo nashine kuma babu wanda yasan abinda dan uwanshi ke yi.

Saidai Vanguard ta ce ta samu labarin cewa, Fashola da Hadiza Bala Usman da Rotimi Amechi da Hadi Sirika duk zasu sake samun matsayin ministocin.

No comments:

Post a Comment