Pages

Sunday 23 June 2019

Copa Amerika: Kwallon da Firmino ya ciwa Brazila a haduwarsu da Peru ta dauki hankula

Tauraron dan kwallon kasar Brazil, Roberto Firmino ya dauki hankula a wasan da kasar tasu ta buga da kasar Peru a ci gaba da gasar cin kofin Copa Amerika da ake yi inda suka lallasa Peru din da ci 5-0.



Casemiro, Firmino, Everton, Alves da Willian ne suka ciwa Brazil kwallayen ta.

Saidai Firminon da ya ci kwallo ta 2 a wasan da aka buga ranar Juma'ar data gabata wanda ya kawar da kanshi gefe lokacin da zai bugata ya dauki hankula. Saida ya yanke golan sannan ya kawar da kai ya buga kwallon cikin raga.

Ko da a Liverpool Firmino ya taba cin irin wannan kwallon.


No comments:

Post a Comment