Pages

Sunday 23 June 2019

'Yan kwallon mata na Najeriya sun yi zaman dirshan a otaldin kasar Faransa sunce ba zasu dawo ba sai an biyasu hakkokinsu

Bayan fitar dasu daga gasar cin kofin Duniya ta mata da kasar Jamus ta yi jiya, Asabar, kungiyar 'yan kwallon mata ta Najeriya, Super Falcon sun yi zaman dirshan a otal din da suke a kasar Faransa inda suka ce ba zasu dawo ba sai an biyasu hakkokinsu da suke bin hukumar kwallon Najeriya tukuna.



Wasu daga cikin 'yan kwallon sun gayawa ESPN cewa, suna bin bashin alawus-alawus tun na wajan shekaru 3 da suka gabata da ba'a biyasu ba da ya kai miliyan 2, an bamu rabi akace wai iya kudin da muke bi kenan, to munaso sai sun biyamu sauran, inji daya ga cikin 'yan kwallon.

Hakanan kuma 'yan kwallon matan na bin bashin alawus-alawus na kowace rana da ake biyansu a gasar cin kofin da suka je kasar Faransar har na tsawon kwana biyar, shima suna so a biyasu kamin su dawo gida.

Hakanan 'yan kwallon sun bukaci a basu rabonsu na kudin da hukumar kwallon kafa ta Duniya ke baiwa kasashen da suka halarci gasar cin kofin Duniyar.

Saidai shugaban hukumar kwallon Najeriya, Amaju Pinnick ya bayyanawa ESPN cewa babu wani bashi da 'yan kwallon suke bi, an biyasu duka kudadensu.

Ya kara da cewa abinda kawai suke binmu shine kasonsu na kudin da FIFA ke baiwa kasashen da suka je gasar cin kofin Duniya wanda kuma ba'a riga aka bayar da kudin ba, sai bayan an kammala gasar ake bayar da kudin. Amma sun nace wai sai mun biyasu, sunce sun yi magana da wasu 'yan kwallon kasashen Kamaru da Faransa sunce musu an biyasu.

A baya dai Super Falcon sun taba yin irin wannan zaman dirshan a otal din da suka sauka bayan kammala gasar da suka halarta saboda bashin alawus-alawus da suke bi da ba'a biyaasu ba

No comments:

Post a Comment