Pages

Monday 24 June 2019

Da na biyewa ta masu bani shawara da tuni ina yaki da kasashen Duniya da dama>>Shugaba Amurka

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa da ya biyewa ta masu bashi shawara da tuni yanzu yana yaki da kasashen Duniya da yawa.



Shugaban wanda a baya tun kamin ya hau mulkin kasar Amurka ansanshi da sukar yake-yaken da kasar take yi inda yake Allah wadai dasu, ya bayyana cewa da ya biyewa ta me bashi shawara akan harkar tsaro, John Bolton da tuni ya kaiwa Iran harin soji.

Kai bama Iran kadai ba da yanzu yana yaki da kasashen Duniya da dama.

Saidai yace maimakon yaki zai yi kokarin ganin an kakabawa kasar ta Iran karin takunkumai masu karya tattalin arziki.

A wani labarin irin wannan kuwa, kasar Rasha ta bayyana cewa bata tare da kasar Amurka wajan kakabawa Iran wani takunkumi kuma koda an saka takunkumin su ba zasu yiwa Iran komai ba.

No comments:

Post a Comment