Pages

Monday 24 June 2019

Gasar cin kofin Duniya na mata: Ingila ta cire Kamaru: Wasa ya jawo cec kuce sosai

Kasar Kamaru tasha kashi a hannun kasar Ingila a wasan da suka buga na ci gaba da neman cin kofin Duniya na mata inda Ingilar ta lallasa Kamaru da ci 3-0.



Saidai wasan ya matukar dauki hankula saboda dambarwar da aka sha da 'yan wasan Kamarun.

Da farkodai Kasar Ingila taci kwallo, sai 'yan kasar Kamarun suka ki yadda inda sukace ai akwai 'yan wasan Ingilar biyu da suka yi satar gida, dan haka kwallon bata ciwu ba, haka akaita daga dasu saikace ana kwallon layi, suka ma hade kai sukaki zuwa a ci gaba da buga kwallon tunda ba'a musu adalci ba, hakan yasa aka bata lokaci tsawon mintuna 3.
Na'urarnan me taimakawa Alkalin wasa, VAR ta nuna cewa kwallon ta ciwu, saidai wasu na ganin cewa rashin sabo da na'urarne yasa 'yan wasan Kamarun yin abinda suka yi.


Wani lamari da ya kara daukar hankulan mutane, duk da cewa alkalin wasan ta kawar da kai shine yanda 'yar wasan Kamaru, Augustine Ejangue ta tofawa 'yar wasan kasar Ingila, Toni Duggan miyau.
Alkalin wasan dai ta kawar dakai daga wannan lamari duk da cewa 'yar wasan ingilar ta jawo hankalinta akai. Haka ta goge miyan aka ci gaba da wasa.

Bayan dawowa daga hutun Rabin lokaci, 'yan matan Kamaru sun saka kwallo a ragar Ingila, saidai Alkalin wasan tace kwallon bata ciwu ba dan kuwa 'yar kwallon na Kamaru ta yi satar gida.

Wannan ma ya jawo wani hargitsin wanda da kyar aka shawo kan Ajara Nchout da ta ci kwallon.

Amma duk da haka saida taita rusa kuka saboda kwallon da aka hanasu, a karshe dai an ci gaba da wasan, saidai wasu 'yan wasan kamarun sun zargi FIFA da nuna wariyar launin fata.
A ganin ido dai kwallon ba satar gida amma na'urarnan dake taimakawa Rafali VAR ta nuna cewa an yi satar gida.

Akwai kuma lamarin nushin da 'yar wasan Kamaru ta wa 'yar kwallon Ingila da shima ya dauki hankula.

Haka dai aka tashi wasan 3-0.

A yanzu dai an cire duka kasashen Afrika da suke a gasar.

No comments:

Post a Comment