Pages

Sunday 23 June 2019

Daya daga cikin Wanda kakakin majalisar dattijai ya baiwa mukami ya ajiye mukamin

Wanda kakakin majalisar dattijai, Lawal Ahmad ya nada a matsayin me bashi shawara akan sabbin kafafen sadarwa, Olu Onemola wanda tsohon na hannun damar tsohon kakakin majalisar ne, Bukola Saraki ya ajiye aikin.



Olu Onemola ya bayyana cewa, dalilin da yasa ya ajiye aikinshi shine irin yanda bashi mukamin ya jawo cece-kuce.  

Amma yana godiya ga Lawal da karramashi da yayi.

Lawal din ya amince da ajiye mukamin na Olu Onemola inda yace yana mai fatan Alheri.

Bayan Festus Adedayo wanda aka yi caa akan mukamin da Lawal ya bashi kuma daga baya ya saukeshi akwai sauran wanda Saraki yayi aiki dasu da Kuma Lawal din shima ya baiwa mukami wanda suma wasu 'yan APC suka bukaci ya sauke su amma ya kiya.

No comments:

Post a Comment