Pages

Sunday 23 June 2019

Manchester United na son sayar da Sanchez amma yaki sayuwa saboda tsadar albashinshi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na neman kai da dan wasanta da ta siyo daga Arsenal dan asalin kasar Chile, watau Alexis Sanchez. 



A yanzu dai rahotanni sun bayyana cewa an buga an buga amma an rasa kungiyar da zata sayi dan wasan da ake biya albashin fan dubu 505 duk sati saboda tsadar shi.

Rahotanni sun bayyana cewa har kungiyoyin kasar China masu kudi sun kasa sayen Sanches din da a gaba dayan kakar wasan data gabata kwallaye 2 kacal ya ciwa Machester United din.

Man U dai na neman sayar da Sanchez me shekaru 30 ne dan ta samu kudin da zata yi cefanen wasu karin 'yan wasa amma har yanzu ya ki shiga.

Wani Rahoto daga Daily Mail ya bayyana cewa Inter Milan na son karbar Sanchez a matsayin aro na tsawon lokaci amma matsalar itace dole Man U ce zata rika biyan rabin albashinshi watau fan 250,000 duk sati.

A gasar da ake bugawa ta neman cin kofin Copa Amerika, Sanchez ya ciwa kasarshi ta Chile kwallaye biyu, hakan yasa aka rika tunanin ya dawo da nuna kwazo yayin da shi kuma yace dama can yana da kwazonshi, amma a Ingila ba'a bashi damane.

No comments:

Post a Comment