Pages

Saturday 15 June 2019

Gwamonin APC 3 da suka fadi zabe a jihohinsu zasu samu mukamin ministoci


Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC ta yanke shawarar sakawa gwamnoninta 3 da suka rasa kujerunsu a babban zaben da ya gabata da mukaman ministoci a zangon mulkin Buhari na biyu.

Gwamonin kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito sune na Legas, Akinwunmi Ambode dana Adamawa, Mohammed Bindow dana Bauchi, Muhammad Abubakar.

Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Ahmad Lawal ya tabbatarwa da Punch wannan labari inda yace duk da cewa har yanzu uwar jam'iyya bata bukaci a mika mata sunayen wanda zasu zama ministoci ba ajihohi amma akwai kyautata zaton cewa tsohon gwamnan Adamawar ne zai samu wannan mukami.

Lawal ya kara da cewa, umarnin uwar jam'iyyar shine duk jihar da gwamnan jam'iyyar yayi rashin nasara to sunanshi ne za'a bayar a matsayin wanda za'a baiwa minista. da wannane ake tunin tsohon gwamnan Bauchi, Muhammad Abubakar da tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Abode zasu samu matsayin ministocin.

No comments:

Post a Comment