Pages

Tuesday 25 June 2019

Mutanen garine ke bamu matsala a yaki da Boko Haram >>Buratai

Shugaban Hafsan soji, Janar Buratai ya bayyana cewa, matsalar yakin da suke yi da Boko Haram da yaki ci yaki cinyewa, mutanen gari ne da basu basu hadin kai.



Buratai ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai shi da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara a jiya Litinin kamar yanda Channels  ta ruwaito.

Buratai ya karyata maganar da ake yadawa wai yace sojoji basa mayar da hankali wajan aikinsu inda yace matsalar na gurin jama'ar gari, saboda suna yakine da wanda basu da fuska, basu da wasu kaya da ake gane su dasu sannan suna sajewa da jama'ar gari.

Yace sukan shiga cikin jama'a su rika kallon yanda ake kawo sojoji kowane garin kamin daga baya su koma su yo shirinsu kawo hari inda suke kashe rayuka da kuma kwasar dukiyoyi.



Yace kuma mutane suna ganin wadannan sabbin fuskoki a cikinsu amma basa iya kaiwa sojojin rahoto. Yace idan dai aka ci ga a da tafiya a haka to kowa zai kasance cikin matsala ne.

Ya bukaci cewa mutane su daina kallon yakin da Boko Haram a matsayin aikin Sojoji kawai, suma suna da gudummuwar da zasu bayar ta hadin kai.

No comments:

Post a Comment