Pages

Wednesday 26 June 2019

'Yan kwallon Najeriya sun yi fushi da kin biyansu hakkinsu

Rahotanni sun bayyana cewa an samu baraka a tawagar 'yan kwallon Najeriya, Super Eagles dake wakiltar Najeriyar a gasar cin kofin nahiyar Afrika dake gudana a kasar Egypt bayan da aka ki biyansu alawus dinsu.




An ruwaito cewa akwai kudin alawus da ya kamata a biya 'yan wasan amma ba'a biyasu ba wannan yasa suka bijirewa shirya ganawa da 'yan jarida da aka yi sannan kuma suka yi latti wajan fitowa yin atisaye.

Ahmed Musa yaki fitowa tattaunawa da 'yan jaridu inda rahotanni suka bayyana cewa ya halarci wani taro namusamman da 'yan wasan ke yi.

Zaka so karanta 'Yan kwallon mata na Najeriya sun yi zaman dirshan a otaldin kasar Faransa sunce ba zasu dawo ba sai an biyasu hakkokinsu


Kocin kungiyar ya bayyana cewa 'yan wasan na shirin daukar mataki amma yana fatan za'a shawo kan matsalar dan fuskantar abonda ke gaba.

A gobene dai ake sa ran Najeriya zata buga wasa da kasar Guinea a ci gaba da gasar.

No comments:

Post a Comment