Pages

Monday 24 June 2019

Neymar ya aikawa da abokanshi a Barcelona sakon cewa kwanannan zai koma kungiyar

Rahotanni dai na kara tabbatar da shirin komawar Neymar tsohuwar kungiyarshi ta Barcelona daga PSG.



Neymar wanda ga dukkan alamu ya fara gajiya da zama a PSG shekaru biyu bayan komawa kungiyar. Wannan baya rasa nasaba da rashin cimma burinshi na komawa kungiyar, watau daukar kofin Champions league da kuma cin kyautar gwarzon dan kwallo ta Ballon d'Or.

Sabbin rahotanni daga The Mirror sun bayyana cewa Neymar ya aikewa abokanshi dake Barcelona, Lionel Messi da Luis Suarez cewa kada su damu zai dawo kungiyar ta Whatsapp.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa PSG din na neman kai da Neymar amma bata so ta fito ta nuna maitarta a fili, musamman ganin cewa kungiyoyi kadanne ke da kudin da zasu iya sayen Neymar din.

Wasu rahotanni a baya dai sun ce Barcelona zata bada wasu 'yan kwallonta hade da kudi dan ganin ta dawo da Neymar din.

No comments:

Post a Comment