Pages

Thursday 20 June 2019

Real Madrid ta sayarwa Atletico Madrid dan wasa

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta sayi dan wasan Real Madrid, Marcos Llorente akan kudi Yuro miliyan 40.



Llorente ya sakawa Atletico Madrid hannu a kwantirakin wasa na shekaru biyar kuma zai wa kungiyar wasane a matsayin madadin dan wasanta, Rodri Hernandez. Akwai kungiyoyi da dama dake son sayen Llorente da kudin mafi tsada amma ya zabi Atletico.

Rahotanni dai sun bayyana cewa tuni dama Zidane ya gayawa dan wasan me shekaru 24 cewa bafa zai yi dashi ba a kakar wasa me zuwa, dalili kenan da ya nemi canjin kungiya.

Masu sharhi dai na ganin cewa Madrid bata so sayarwa da Atletico Madrid da dan wasan ba ganin cewa ita ta raineshi, ta so ace wata kungiyace ba ta Laliga ba zata sayi matashin dan wasan saidai shi kuma Llorente ya fi son Atletico Madrid dan haka dole Madrid din suka sayar dashi kuma suma dama suna bukatar kudi ganin yanda suke sayen 'yan wasa babu kakkautawa.

No comments:

Post a Comment