Pages

Wednesday 26 June 2019

Soja Ya Harbe Dan Sanda A Jihar Borno

Wannan jami'in 'yan sandan Nijeriya ne, yana bangaren masu yaki da ayyukan ta'addanci, Police Counter Terrorist Unit (CTU) a jihar Borno


Jiya tsautsayi ya rutsa da shi wani gurbataccen jami'in sojan Nijeriya ya harbe shi da bindiga a garin Maiduguri, kuma ya gudu, shi kuma ya fadi ya mutu nan take. Ya mutu ya bar mata da 'ya'yansa. 'Dan jihar Bauchi ne.

Ku nemawa Usman rahama a gurin Allah, Allah Ya yafe masa kura-kuransa, Allah Ya saka masa da Aljanna. Amin.

Daga Datti Assalafiy


No comments:

Post a Comment