Pages

Friday 21 June 2019

Yau ake bude gasar cin kofin kasashen Afrika a Masar

Yau ake fara gudanar da babbar gasar cin kofin kasashen Afrika, inda Masar mai masaukin baki za ta fara wasan bude fage da Zimbabwe, yayinda hankula za su karkata kan Mohamed Salah dan asalin Masar da ke taka leda a Liverpool.



A karon farko kasashen Afrika 24 ne ke fafatawa a wannan gasa wadda manazarta ke cewa, akwai yiwuwar Masar ta sake lashe gasar a karo na takwas duk da cewa, za ta fuskanci gagarumin kalubale daga takwarorinta.

Mahukuntan gasar sun ce, an tanadi abubuwan da ake bukata na gudanar da gasar cikin armashi duk da dai Masar ta samu izinin karbar bakwancin ne a daidai lokacin da ya rage watanni shida a fara gasar.

A gobe Asabar ne, Najeriya za ta fara wasanta na farko a rukuninta na B kuma za ta hadu ne da Burundi wadda a karon farko kenan da ta samu damar shiga a dama da ita a gasar.

Tsoffin ‘yan wasan Super Eagles irinsu Mutiu Adepoju sun shawarci ‘yan wasan na Najeriya da su guji yi wa Burundi kallon raini domin kuwa tana iya bada mamaki duk da cewa, jinjira ce a gasar ta AFCON.

A bangare guda, za a bude gasar ce ta cin kofin Afrika kwanaki kalilan da mutuwar tsohon shugaban kasar Masar, Mohamed Morsi.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment