Pages

Friday 21 June 2019

ZABEN 2023: Dole Shugabancin Kasa Ya Tsaya A Arewa>>Matasan Arewa

Gamayyar Kungiyar cigaban matasan yankin Arewacin Najeriya 19 sun bayyana cewar ya zama wajibi a yankin Arewa ya sake fitar da Shugaban Kasa a shekarar 2023 idan Buhari ya kammala wa'adin mulkin shi.


Matasan na Arewa sun tabbatar da cewa, babu wani tagomashi da 'yan Arewa suka samu a karkashin shugabancin Buhari illa zubar da jini da talauci gami da garkuwa da mutane, saboda haka a mulkin Buhari Arewa ba ta da wakilcin komai, a domin haka lallai ne mulkin ya tsaya Arewa a shekarar 2023.

Ƙungiyar ta dauki  wannan  matsaya  ne a yayin wata ganawa da Shugaban Ƙungiyar na kasa Alhaji Yerima Shettima ya yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Shugaban matasan Arewan ya kara da cewar ko shakka babu APC za ta mutu kafin shekarar 2023, domin abin da ke rike da APC dama shine Buhari, kuma bukatar Buhari ta cika na yin shugabancin kasa har sau biyu, saboda haka bai da wani buri da jam'iyyar a yanzu, ba zai yi takara a 2023 ba, bisa ga haka 'Yan Arewa na da damar zaben wanda ya dace kuma wanda zai kai yankin Arewa da kasa gaba.

Dangane da ko waye Matasan na Arewa zasu marawa baya a zaben 2023? Shugaban matasan Arewa na Arewa ya ce a yanzu haka dai basu da wani dan takarar da suke goyon baya har sai idan lokaci ya yi masu neman kujerar sun fara fitowa, amma duk da haka yana tabbatar wa jama'a cewa ko kadan ba za su rungume hannu suna kallon ana cutar da yankin Arewa ba, za suyi gwagwarmaya iyakar karfin su domin ceto yankin Arewa.

Matasan wadanda suka jajantawa jama'ar Arewa dangane da abin da suka kira iftila'i da mulkin Buhari ya jefa su a ciki, kuma ko kadan ba za su yarda da yunkurin da Tinubu ya ke yi na ganin ya zama shugaban kasa ba, dole za suyi tsayuwa irin ta mai daka domin ganin mulki ya cigaba a Arewa a 2023.


No comments:

Post a Comment