Pages

Wednesday 17 July 2019

Ban caccaki gwamnatin Buhari ba, Karya aka min>>Farfesa Wole Soyinka

Shahararren marubucinnan Farfesa Wole Soyinka ya fito ya karyata maganar da akace yayi ta caccakar gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda aka ruwaito cewa yace hare-haren fulani makiyaya sun shafe nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.



A martanin daya fitar ga manema labarai yace, Yayi mamakin yanda babbar jarida irin The Nation zata mai karya. Shi baice Hare-haren fulani makiyaya sun goge nasarorin gwamnatin Buhari ba.

Abinda yasan anyi shine wasu yara 'yan makaranta sun zo mai taya murnar cika shekaru 85 sannan aka bukaci yayi magana akan gwamnatocin Najeriya kuma abinda ya fada shine mulki ba abune me sauki ba, musamman mulkin kasa irin Najeriya.

No comments:

Post a Comment