Pages

Wednesday 17 July 2019

Bayan arangama da 'yansanda, 'yan shi'a sun sake fitowa zanga-zanga

Bayan arangamar da suka yi da 'yansansa a makon daya gabata a babban birnin tarayya, Abuja, 'yan shi'a sun sake fitowa zanga-zangar neman a saki shugabansu,Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a Abuja ranar Talata.



Me magana da yawun kungiyar, Abdullahi Musa ya bayyana cewa ba zasu daina fitowa ba har sai an saki Zakzaky.

A Kaduna ma, 'yan shi'ar sun fito Zanga-Zanga inda suka yi arangama da 'yansanda suka buga musu barkokon tsohuwa, saidai Rahotanni sun bayyana cewa 'yan shi'ar basu guduba inda suka bi 'yansandan da gudu.
Babban lauya kuma dan rajin kare hakkin biladama, Femi Falana ya gargadu gwamnatin tarayya akan 'yan shi'a inda yace zata iya sake kirkirar wasu sabbin 'yan ta'adda.

No comments:

Post a Comment