Pages

Tuesday 16 July 2019

Dole Mu Kawo Karshen Bara A Jihar Kano>>Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dk. Abdullahi Ganduje ya sake jaddada manufar gwamnatinsa na ganin ta kawo karshe barace-barace a jihar Kano. Gwamnan ya ce za su tabbatar sun dakile bara da hana Almajirai yawo a tituna suna neman abin da za su ci a fadin jihar.


Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yiwa shugaban majalisar masu rinjaye, Alhaji Alhassan Ado Doguwa da sauran al’ummar Yankinsa, wadanda suka kawo wa gwamnan ziyara a gidan gwamnatin Kano a ranar Lahadi.


No comments:

Post a Comment