Pages

Friday 19 July 2019

Hattara: Wasu na amfani da hotunan 'yan fim suna yaudarar mutane


Masu yaudarar mutane dan rabasu da kudinsu ta hanyar karyar cewa ka basu kudi zasu ninka maka su nan da wani lokaci sun fito da dabarar yin amfani da hotunan jaruman fina-finan Hausa.

Wasu daga cikin 'yan masana'antarne suka fito dan gargadin mutane akan wannan sabon lamari.

Malam Aminu Saira wanda shahararren me bayar da umarnine a masana'antar ya fito ta shafinshi na Instagram inda ya gargadi mutane da su gujewa masu saka hotunan 'yan fim suna cewa su kawo kudi wai za'a ninka musu.

Ya bayyana cewa basu da alaka da irin wadancan mutane.

Hakanan itama Mansurah Isah ta gargadi mutane da su guji baiwa masu saka hotunan 'yan fim suna cewa a basu kudi dan su juyawa mutum su bashi riba inda tace damfarane ba gaskiya bane.

No comments:

Post a Comment