Pages

Monday 8 July 2019

Komawar Neymar Barcelona ta hadu da cikas bayan da PSG ta bukaci ya ci gaba da mata wasa

Rahotanni sun bayyana cewq komawar tauraron kasar Brazil dake bugawa kungiyar PSG wasa, Neymar tsohuwar kungiyarshi ta Barcelona ta samu matsala bayan da PSG ta bukaci ya ci gaba da buga mata wasa.



Rahotanni dai sun bayyana a baya cewa Neymar din ya gaji da zama a PSG kuma yana yin dukkan me yiyuwa wajan ganin ya koma tsohuwar kungiyarshi ta Barcelona.

Saidai wani sabon rahoto daga Telefoot na cewa PSG ta bukaci Neymar da ya mutunta alkawalin da ya saka wa hannu na buga mata wasa wanda sai nan da shekaru 3 zai kare sannan nan da sati daya ake sa ran Neymar din zai koma yin Atisaye a kungiyar bayan rashi lafiya ta hanashi bugawa Brazil gasar Copa Amerika.

Sau biyu dai rahotanni suka bayyana cewa anawa Real Madrid tayin Neymar amma ta ki amincewa saboda tsadarshi.

No comments:

Post a Comment