Pages

Wednesday 21 August 2019

Bayan barar da bugun daga kai sai Gola da Pogba yayi: Kocin Man United ya fitar da dan wasan da zai rika bugawa kungiyar Fenareti

A ranar litinin din data gabatane da dare a wasan da Manchester United ta buga da kungiyar Wolves wanda ya kare da sakamakon kunnen doki watau 1-1, tauraron dan kwallon Man United Paul Pogba ya samu bugun daga kai sai gola, ya buga amma ya barar da ita.




Kamin buga kwallon, an ga Pogba da Marcus Rashford sun dan yi magana sannan ya buga.

Barar da bugun Fenaretin ya jawo cece-kuce sosai inda har aka samu wasu suka farawa Pogban cin zarafin wariyar launin fata a shafukan sada zumunta data kai ga har abokin wasanshi Maguire yayi kira da a dauki mataki.

Bayan tashi daga wasan sai da me horas da kungiyar Man United, Ole Gunnar Solskjaer ya tattauna batun da Rashford da Pogba a dakin canja kaya.

Kuma rahotannin dake fitowa daga jaridar The Sun ta kasar Ingila na cewa Ole Gunner ya yanke hukunci kan cewa daga yanzu Rashford ne zai rika bugawa Man United bugun daga kai sai me tsaron gida dan gudun sake samun matsala irin wannan.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment