Pages

Friday 23 August 2019

BAYAN KORA: An gurfanar da ’yan sanda hudu da suka kashe masu laifi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kori ‘yan sanda hudu da aka samu da bindige wasu mutane biyu da ake zargi da laifin satar wayar hannu.


Wadanda da aka kora din sun hada Fabiyi Omomayara, Olanikyi Solomon, Solomon Sunday da kuma Aliyu Mukaila.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Legas, Bala Elkana ne ya bayyana haka yau Alahamis a cikin wata takardar da aka raba wa manema labarai a Legas.

Ya ce tuni aka ingiza keyar su zuwa kurkuku bayan an kore su daga aikin dan sanda gaba daya.

An kore su ne bayan sun kashe wasu da ake zargi masu laifi ne, da suka kamo a Iba, Legas.

An kama wadanda ake zargin su biyu ne bisa zargin satar waya mai tsada, samfurin iPhone da aka kiyasta kudin ta ya kai naira 450,000.

Kwamishinan ’yan Sanda na Legas, Zubairu Mu’azu ne bada umarnin gaggauta binciken su, bayan da aka rika watsa bidiyon yadda aka kashe wadanda aka kamo din su biyu.

An same su da laifin kisan ne bayan an kammala bincike, sannan aka gurfanar da su kotu, inda aka caje su da tuhumar aikata kisa.

An gurfanar da su ne a kotun Majistare ta 5 da ke Ebute Meta, Legas a yau Alhamis.

An dage sauraren karar su zuwa ranar 23 Ga Satumba.
Premiumtimeshausa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment