Pages

Saturday 17 August 2019

JANAR BABANGIDA A SHEKARU 78

Wasu Daga Cikin Ayyuka Dubu Da Ya Yi A  Kasar Nan

Shugaba Babangida Ne Aka Taba Samu Ya Aikata Ayyukan Alheri Masu Amfani Har Guda 1,000 A Zamanin Mulkinsa Na Shekaru Takwas, Inda Bayan Shugaba Babangidan, Babu Koda Wani Shugaba Guda A Duk Tarihin Nahiyar Afirka, Da Kuma Tarihin Kafatanin Shugabannin Da Suka Taba Ko Kuwa Suke Kan Kujerar Shugabancin 'Kasashensu A Halin Yanzu, Wanda Ya Kwatanta Haka, Idan Banda KBE da Sir Ahmadu Bello Sardauna Ya Gina Kuma Ya Samar Da Ayyukan Alheri Guda Dari, A Fadin Yankin Arewa; Ahmadu Bello University Zaria, Daya Kenan Na Sardaunan, Sai Kuma Wasu Guda 99 Da Yawancinsu Gwamnonin Arewa Goma Sha Tara Sun Yi Watsi Da Su, Inda Haka Ya Sa Suka 'Bal'balce, Yayin Da Suka Siyar Da Wasu; Irinsu Bank Of The North!


Ga Jerin wasu Ayyukan Alher Na IBB:-

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ne Ya Gina Villa Abuja kuma ya soma tarewa a cikinta, Shi Ne Ya Samar Da Gine-Ginen: Eagle Square, Federal Secretariat, FCDA Secretariat, National Mosque, National Church, National Assembly, Supreme Court, Court of Appeal, Barrack Guda Goma A Abuja, Wuse Market, NNPC Tower.

Shugaba Babangida Ne Ya Samar Da Irin Su:- NAFDAC, DIFRRI, MAMSER (NOA), CCT, CCB, CCN, Gifted Children's School, Suleja, NHIS, NEXIM, NDIC, NDLEA, FRSC, ECOMOG, Ministry of Women Affairs, NWC, National Mathematical Center, NDE, Ministry of Agriculture & Rural Development, NAFSESS, NSFCP, FUMTP, NPB, FEPA, NALDA, CDS, RMRC, CMEWS, NEPC, FMIDS, Petro-Chemical Plant, Kaduna, Petro-Chemical Plant, Eleme, Osaka Dam, Ajaokuta, Shiroro Hydro Power Station, Niger, Dukkanin Sakatariyoyin Gwamnatocin Jihohin Najeriya, Da Kuma Kafatanin Sakatariyoyin Da Yanzu Haka Ake Amfani Da Su A Kowace karamar hukuma, Delta IX Gas Turbine Plant, Bai Taba Siyo Tataccen Man Fetur Daga Wata Kasar Waje Ba, Duk Man Fetur Din Da Aka Sha Zamanin Mulkinsa, A matatun man da Nijeriya Ke Da Su Aka Tace Shi, Duk matatun man Nijeriya Suna Aiki 100% A Sanda Ya Sauka Daga Karagar Mulki.

Shugaba Babangida Ne Ya Kirkiro Jihohi Goma Sha Uku, A Duk Fadin Nijeriya, Inda Kafin Hakan, Da Kuma Bayan Hakan, Babu Wani Shugaban Nijeriya, Wanda Ya Girmama Al'umma, Ta Hanyar Maida Garuruwansu Su Koma Jihohi, Don Kowa Ya Samu 'Yanci, Amfanin Gwamnati Ya Zo Kusa. Ga Jerin Jihohin Da Ya 'Kirkiro Kamar Haka:

Jihar Adamawa.

Jihar Katsina.

Jihar Jigawa.

Jihar Yobe.

Jihar Kebbi.

Jihar Delta.

Jihar Edo.

Jihar Taraba.

Jihar Kogi.

Jihar Abia.

Jihar Osun.

Jihar Enugu.

Jihar Akwa Ibom.

Shugaba Babangida Ne Ya Yawaita kananan hukumomi Har Yawansu Ya Kai 774, Babu Mamaki Kai Da Ke Karanta Rubutun Nan, Idan Ba Domin Hakan Da IBB Ya Yi Ba, Da Wata'kin Har Yanzu Jiharku Babu Ita A Jerin Jihohin Najeriya Da Muke Da Su A Yanzu, Haka Nan Kuma, Da Yanzu Kana Cikin Wata karamar hukuma Ne A Jone, Amma Sai Ga Shi Saboda Kishin Ci Gaban Rayuwarka IBB 'Din Da Babu Mamaki Har Da Kai Ake Zama Ana Cin Mutuncinsa Da Zaginsa, Shi Ne Dai Mai Kaunarka, Tunda Ga Shi Nan Ya Kirkiro Muku jihar Da karamar hukuma Wanda Hakan Ce Ma Ta Ba Ka Damar Samun Bakin Magana!
.
Shugaba Babangida Ya Bar Dollar Amurka Kan Farashin ₦18, Sannan Ba A Ta'ba Ganin Layin Man-Fetur Ba, Koda Kuwa Sau 'Daya Ne, Duk A Tsawon Watanni 96 Da Ya Yi, Yana Mulkar Najeriya. Shi Ne Shugaban Da Ya Fara Samar Da Boreholes A 'Kauyukan Da Pipes 'Din Famfo Bai 'Karasa Ba, Har Ila Yau, A Zamanin Mulkinsa Ne 'Yan Najeriya Da Suka Ga Ruwan Famfo A Ko'ina Ba Wahala, Sai Mutum Ya Bud'e Ya Kunna Ya Yi Amfani Da Shi, Idan Ya Gama Sai Ya Yi Tafiyarsa Ya Bar Kan Famfon A Kunne Yana Ta Zubar Da Ruwa A Banza, Saboda Irin Yadda IBB Ya Jajirce Ya Tabbatar Da Ganin Ruwan Famfon Ya Wadaci Kowa, Kuma Ya Shiga Kowane Lungu Da Sa'ko!

Amma A Haka Ne Muke Zagin IBB 'Din.

Daga Khalid Abdullahi Zaria







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment