Pages

Saturday 17 August 2019

Wasu Daliban Jami'ar ABU Dake Zaria Su Biyu Sun Tsinci Naira Milyan 2.5 Na Wani Lakcara Sun Maida Masa

Wasu daliban jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, masu suna Ahmed Suleiman da Ahmed Usman wadanda aka tura Kwalejin Ilmi dake garin Kontagora jihar Neja sun maidawa wani mutum mai suna Malam Muhammad Kudu Ibrahim kudinsa naira milyan 2.5 da suka tsinta a ranar Larabar da ta gabata.


Kudu Ibrahim, wanda ya yarda da kudin, Lakcara ne a sashen zane da kimiyya na kwalejin ilmi na garin Kontagora.

Daya daliban ya ce sun tsinci kudin ne a cikin wata leda.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment