Pages

Thursday 22 August 2019

Kungiyoyin kare muradun Inyamurai da yarbawa sun koka saboda Buhari ya baiwa yankin Arewa maso Yamma mukaman manyan ministoci 9

Bayan bayyana ma'aikatun da sabbin ministocin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi, jiya,Laraba bayan ya rantsar dasu, kungiyoyin kare murafun Yarbawa, Afenifere dana kare murafun Inyamurai, Ohanaeze sun koka akan cewa shugaba Buharin ya nuna bangaranci.



Kungiyoyin sunce shugaba Buhari ya baiwa yankin Arewa maso gabas inda daga nanne ya fito mukaman manyan ministoci fiye da kowane yanki na kasarnan. Sun kara da cewa Ministoci 9 shugaba Buharin ya baiwa manyan ministoci daga yankin daya hada da jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Zamafara, Jigawa da Sakkwato.

Daga cikin ministocin da suka samu manyan minitoci akwai,Majo Janar Bashir Salihi Magashi daga Kano daya samu Ministan Tsaro da Hadi Sirika daga Katsina daya samu Ministan Sufurin jiragen sama, da Zainab Ahmad da ta samu ministan kudi, Da Muhammad Mahmood daya samu ministan Muhalli da Sulaiman Adamu daga Jigawa daga samu ministan albarkatun ruwa da Sabo Nanono daya samu ministan Noma da Abubakar Malami daga jihar Kevbi daya samu ministan Shari'a, sai kuma Maigari Dingyadi daga Sakkwato daya samu ministan 'Yansanda da kuma Sa'diya Umar Faruk daga Zamfara data samu ministar tallafawa Al'umma da kula da ibtila'i da kuma ragewa jama'a radadin talauci.

Sakataren watsa labaran kungiyar kare muradun yarbawa, Yinka Odumakin ya bayyana cewa wannan mukamai da shugaba Buhari ya tattara har guda tara ya baiwa yankin da ya fito na Arewa maso gabas manyan ministoci ya nuna cewa gwamnatinshi ta bangarancine.

Kuma mataki na gaban da ya wa mutane alkawari kenan.

Shima sakataren kungiyar kare muradun iyamurai ta Ohanaeze, Uche Achi ya bayyana cewa dama abinda suka yi tsammanin shugaba Buhari zai yi kenan dan haka ba su yi mamaki ba saboda tun a baya ya bayyana cewa zai fifita wanda suka bashi kuri'u da yawa fiye da wanda basu bashi kuri'u da yawa ba.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment