Pages

Thursday 22 August 2019

Messi zai buga wa Barca wasa da Betis

Lionel Messi ya kara karfafa gwiwar Barcelona, bayan da ya koma yin atisaye tare da kungiyar ranar Laraba.


Bayan da dan wasan ya ji sauki daga jinyar da ya yi, ya yi atisaye shi kadai a safiyar Laraba, sannan ya yi tare da 'yan wasa da yammacin Larabar.

Hakan ne ya sa kungiyar ke sa ran zai buga mata wasan gasar cin kofin La Liga mako na biyu da za ta fafata da Real Betis ranar Lahadi.

Messi kyaftin din tawagar Argentina ya yi rauni ne a Barcelona lokacin da ya koma daga hutun buga gasar Copa America, wanda Brazil ta zama zakara a gidanta.

Raunin da ya ji ya hana dan kwallon bin kungiyar wasannin atisayen da ta buga na tunkakar kakar da aka fara makon da ya wuce.

Dawowar kyaftin Messi zai kara karfin kungiyar ganinn cewar Luis Suarez zai yi jinyar wata daya, bayan raunin da ya yi a karawa da Bilbao a wasan makon farko.

Haka shima Ousmane Dembele zai yi jinya da ake cewa ta mako shida kafin ya murmure ya dawo buga wa Barcelona tamaula kamar yadda ya kamata.

Saboda haka a 'yan wasan gaba Antoine Griezmann da Rahinha da Carles Perez sune ke cikin koshin lafiya da koci zai iya zaben wanda ya kamata ya yi masa wasa.

Karancin 'yan wasan gaba a Barcelona ya kara rura wutar jita-jita cewar Paris Saint-Germain za ta bari Neymar ya koma Camp Nou kan a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a Spaniya ranar 2 ga watan Satumba.
BBChausa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment