Pages

Thursday 22 August 2019

Ni ba me garkuwa da mutane bane>> inji Wadume da yayi sanadiyyar mutuwar 'yansanda

Hamshakin attajiri kuma wanda aka danganta samun kudinsa da irin yadda ya ke karbar kudaden fansa daga mutanen da yayi garkuwa da su ya karyata ‘yan sanda cewa wai shi ba mai garkuwa da mutane ne.


Waduma ya bayyana wa ‘yan sanda a hukumar ‘yan sanda ta kasa cewa bai taba yin garkuwa da wani.

” Ni dai ba mai yin garkuwa da mutane bane. Aiki na shine in damfari mutane ta hanyar cewa zan samo musu asiri domin wani harka ta su. Anan ne nake damfarar su har na tara makudan kudi.

Duk da cewa ‘yan sanda sun tilasta masa ya amince cewa shi mai yin garkuwa da mutane ne, Wadume ya ce babu abin da ya hada shi da haka.

Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne rundunar ‘yan sanda suka bayyana Wadume a gaban manema labarai inda ya fadi yadda Sojoji suka kashe ‘yan sanda suka sake shi.

Bayanin da ya yi wa jami’an ‘yan sanda a ranar Talata ya yi daidai da zargin da ‘yan sanda suka yi cewa sojoji ne suka bude musu wuta domin su hana a kama Hamisu Wadume ne, wanda ake zargin cewa da sani wasu jami’an sojoji kuma da daurin gindin su ya ke yin garkuwa da mutane.

Wadume wanda ya yi bayani da Hausa, ya ce sojoji ne suka kwance masa ankwa bayan sun kashe ‘yan sandan da suka kamo shi, sannan suka bar shi ya tsere.

“Tun lokacin da na tsere ina boye ne a wani wuri, har zuwa yanzu da ‘yan sanda suka sake kamo ni.” Inji Hamisu.

An kama Hamisu Wadume a Jihar Kano, kamar yadda jan sanda suka bayyana.

Sufeto Janar Muhammed Adamu ya bayyana cewa kama Wadume zai iya bada nasarar kama wasu gungun masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment