Pages

Monday 19 August 2019

Wanda adawar siyasa ta rufewa idone kawai basa ganin aikin da muke yi>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jagoranci bude taron baiwa Sabbin ministocin daya nada da sakatarorin manyan ma'aikatan gwamnati horon aiki yau a babban birnin tarayya, Abuja.




Shugaban ya hori ministocin da cewa zasu yi aikine da kare muadun gwamnati a ma'aikatun da aka basu musamman wajan fitar da 'ya  Najeriya daga kangjn talauci, shugaban ya kara da cewa a karshen mulkinshi Najeriya zata kasance akan hanyar kawar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.

Ya bukaci ministocin da su hada kai dan aiki tare da abokan aikinsu.

A zahiri yake ci gaban da suka kawowa Najeriya wajan yaki da cin hanci, samar ababen more rayuwa da yin kokari kan matsalar tsaro.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment