Pages

Monday 19 August 2019

Gwamna Badaru Ya Wakilci Nijeriya A Kasar Turkiya

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar wanda ke wakiltar Nijeriya a wajen taron noman ridi na duniya da ake yi a Istanbul, babban birnin kasar Turkiya, ya gabatar da jawabin sa ga wakilan duniya.



Ku tuna cewa Jihar Jigawa ita ce ta zamanto ja gaba a kasar nan wajen nooman ridi, wanda hakan ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Gwamnan Jihar domin ya wakilci Kasar a wajen taron.


Da yake gabatar da jawabin nasa Gwamnan wanda aka gabatar da shi a wajen a matsayin shugaban kwamitin tattalin arziki da bai shafi man fetur ba a Nakeriya, ya bayyan yadda Najeriya ta zage dantse wajen harkokin noman ridi, inda ya bada bayani game da yadda Gwamnati ke tallafawa manoma musamma karkashin tsarin noman kulasta wanda ya dora harkar noman a kan tafarki nagari a Jihar jigawa dama kasa baki daya.

Daga karshen jawabin nasa, Gwamnan ya yi kira ga masu saka hannun jari da su garzayo Jihar jigawa domin su anfana da harkar noman ridi.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment