Pages

Wednesday 21 August 2019

Wata kila in yi ritaya daga buga kwallo shekara me zuwa>>Ronaldo


Ronaldo Zan iya kaimwa miliyan 300
Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya bayyana damuwa akan yanda ake tsugawa 'yan kwallo kudi a yanzu koda kuwa dan wasa be nuna wata bajinta ba sai kaga an saka mai miliyan 100.



Ronaldo wanda Juventus ta sayo daga Real Madrid akan Yuro miliyan 112, Neymar, Mbappe, Joao Felix, Antoine Griezzmann da Philippe Coutinho ne kawai suka fishi tsada.

"Kasuwar wasanni ta canja matuka, inji Ronaldo, yanzu ka duba kowane dan wasa sai kaji ance Yuro miliyan 100 koda kuwa ba gwani bane" Inji Ronaldo.

A shekarar 2009 ne Ronaldo ya koma Real Madrid daga kungiyar Manchester United a matsayin dan kwallo mafi tsada a Duniya kan kudi Yuro miliyan 94.

Da aka tambayeshi inda ace yanzu yana dan shekaru 25 nawa yake ganin za'a iya sayar dashi?

Sai Ronaldo ya kada baki yace idan dai za'a sayar da gola akan Yuro miliyan 75 to dan kwallon da ya yi irin abinda nayi na bajinta za'a iya sayar dashi kusan ninki 4 na wannan kudin. Wajan Yuro miliyan 300 kenan.

"Amma ni wannan be dameni ba" Ronaldo ya gayawa TVI.

Da aka tambayi dan shekaru 34 ko yaushe yake tunanin dena buga kwallo?

Sai ya kada baki yace bashi da tabbacin sanda zai dena dan kuwa yana iya kasancewa shekara me zuwa ko kuma zai iya kai shekaru 40 zuwa 41 yana kwallo.

"Badai zan iya cewa ga takamaiman lokacin da zan dena kwallo ba amma ina kokarin jin dadin ci gaba da jan zarena a yanzu" injishi.

Ronado ya kuma yi abinda aka sanshi dashi, watau cika baki in yace

"Shin akwai dan kwallon kafa da ya taba kafa irin tarihin dana kafa?"

"Bana tunanin akwai dan kwallon da ya fini kafa tarihi"




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment