Pages

Wednesday 21 August 2019

Wani dan ta'adda da aka kama a jihar Katsina ya bayar da labarin yanda jirgin sama ke kai musu makamai


Wani matashi dan shekaru 20 da aka kama cikin wanda ake zargi da ayyukan ta'addanci a jihar Katsina me suna Aliyu Musa ya bayyanawa manema labarai cewa ya taba ganin wani jirgi me saukar angulu ya kawowa me gidansu makamai a dajin Dinya dake karamar hukumar Kankara jihar Katsina.

Musa tare da Salmanu Isa dan shekaru 18 na daga cikin wanda aka kama da zargin ayyukan ta'addanci aka kuma gabatar dasu ga manema labarai a hedikwatar 'yansanda ta jihar Katsina,kamar yanda Punch ta ruwaito.

Musa ya bayyana cewa da jirgin yazo ogansu ne kawai yaje inda yake sannan wani mutum daga cikin jirgin ya wurgo mai makamai inda daga baya aka basu suke aika-aika dasu.

Musa ya kara da cewa a hare-haren da suka kai ya kashe a kalla mutane 5 kuma ana biyanshi dubu 17 a duk harin da suka kai.

Ya kara da cewa saidai shugaban nasu ya tsere ba'a kamashi ba.

Me magana da yawun rundunar 'yansandan jihar ta Katsina, ASP Anas Gezawa ya bayyana cewa, gugun su Musa sun kashe mutane akalla 25 tare da kwace shanu da dama saidai yace ana ci gaba da bincike.






Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment