Pages

Saturday 17 August 2019

'Yan Kannywood suna Allah-wadai da kama Sanusi Oscar

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, suna ci gaba da yin Allah-wadai da kama wani abokin aikinsu wato Darakta Sanusi Oscar.


Jarumi Misbahu M Ahmad ya wallafa wani bidiyo inda yake bayyana bacin ransa ga Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma'ila Na'abba Afakallahu a shafinsa na Instagram, yana mai cewa siyasa ce ta sa aka kama shi.

Sai dai Afakallahu ya shaida wa BBC cewa an kama Oscar ne, wanda yana cikin 'yan fim din da ke goyon bayan Kwankwasiyya, saboda ya "saba ka'idojin gudanar da sana'arsa a Kano, inda ya saki wata waka wadda akwai badala a ciki".




Ya kara da cewa sun jima suna bibiyar Oscar domin su kama shi, amma sai a 'yan kwanakin nan ne suka samu damar yin hakan.

Tuni dai aka gabatar da Oscar a gaban wata kotu a Kano, ana tuhumarsa da yada batsa.

Kusan yawancin 'yan fim din sun rabu gida biyu - masu goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki da kuma bangaren hamayya na PDP (wato Kwankwasiyya a Kano), kuma siyasa kan fito fili a wasu ayyukansu.


Shi ma fitaccen jarumin fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango, yana daya daga cikin mutanen da suka fara bayyana bacin ransu dangane da batun.

Abin da ya sa shi fita daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.

Jarumi Mustapha Nabraska shi ma ya bayyana cewa ya daina wasan Hausa saboda kama abokin aikinsu.

Sai dai Sani Danja ya bukaci a warware matsalar ta hanyar maslaha, "ba tare da cin zarafin mutum ba," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram.


Ya ce kama Oscar "ba daidai ba ne," hakazalika ya bukaci duka 'yan Kannywood da su dauki kansu a matsayin 'yan uwan juna kuma su kasance tsintsiya madaurinki daya.

Ita ma shahararriyar jarumar Kate Henshaw wacce take fitowa a fina-finan kudancin Najeriya wato Nollywood, ta yi Allah-wadai da kama daraktan, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram.
BBChausa.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment