Pages

Monday 19 August 2019

'Yan uwanmu Inyamurai na shiga rigar fulani suna kisa da satar mutane dan kudin fansa>>Inji kungiyar kare muradun Inyamurai

Kungiyar kare muradun inyamurai ta Ohanaeze ta fito ta bayyana cewa wasu Inyamuran a yakin kudu maso gabas na shiga rigar fulani dan sace mutabe dan kudin fansa da kuma kisan ba gaira ba dalili.



Shugaban kungiyar, Chief Nnia Nwodo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Yace an kama wasu masu laifi da suka kashe wasu limaman coci biyu kuma sun amsa laifukansu, kungiyar ta lura da cewa wasu inyamurai na amfani da rikicin fulani suna shiga rigqr fulanin dan aikata kashe-kashe da satar mutane dan kudin fansa.

Dan haka yake kira ga sarakunan gargajiya da wakilan al'umma da su nemo irin wadannan bata gari su damkawa hukuma dan maganin su.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment