Pages

Friday 18 October 2019

A karshe dai Gwamnatin tarayya ta bayyana abinda ta yi da kudin data kwace daga barayin gwamnati

Bayan da 'yan Najeriya suka jima suna tambayar shin wai yaya aka yi da kudaden da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta kwato daga hannin barayin gwamnati? A karshe dai gwamnatin ta yi bayani.




Me baiwa shugaban kasar Shawara akan harkar yaki da rashawa Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa yawan kudin da EFCC ta kwace sun kai Naira Tiriliyan daya kuma a shekarar 2017 ta yi amfani da rabin kudin wajan shirin tallafawa Al'umma.

Hakanan a shekarar 2018 ma an yi amfani da sauran rabin wajan irin wannan aiki da kuma wasu ayyuka a kasafin kudi.

Hadiza Bala Usman wadda tana cikin masu baiwa shugaban shawara akan yaki da Rashawa ta bayyana cewa suna baiwa shugaban shawarar ya kafa wata hukuma ta daban wadda zai zama aikinta kawai shine sayar da kayan da EFCC din ta kwato maimakon ace EFCC itace zata kwato kayan kuma ta sayar dasu da kanta



Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment