Pages

Friday 18 October 2019

Kashi 80 cikin 100 na kudin da aka baiwa 'yan Najeriya tallafi daga Kudin da aka kwace na satar da Abacha yayi ne aka samosu>>Gwannatin tarayya

Me baiwa shufaban kasa shawara kan tallafawa al'umma Mrs Maryam Uwais ta bayyana cewa kashi 80 na tallafin da aka baiwa Najeriya an yi amfanine da kudin da aka kwace wanda ake zargin tsohon shugaban kasa,Sani Abacha da sacewa.




Ta kara da cewa sauran kashi 20 din an sameshine daga bashin da aka ciwo daga bankin Duniya.

Maryam ta yi wannan bayanine a wajan wani taro da aka yi a babban birnin tarayya, Abuja kan kwato kadarori da kudin gwamnati da aka yi sama da fadi dasu.

Ta kara da cewa mutane 18,200 ne suka karbi bashin kuma kasa da 1000 ne kawai suka kasa biyan bashin.

Tace tsarin ya bada sakamakon da ake so dan kuwa wadanda suka karbi bashin na tin kasuwanci da harkar Noma.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment