Pages

Thursday 17 October 2019

Akwai kungiyoyin agajin da ke wa Boko Haram aiki>>Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Shiyyar Barno ta Kudu, ya bayyana cewa akwai wasu kungiyoyin agaji da ke taimakon Boko Haram a Jihar Barno.


Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Majalisar Dattawa, jiya Talata.

Ndume wanda shi ne Shugaban Kwamitin Lura da Ayyukan Sojoji, kwanan nan ya dawo daga jizarar gani-da-idon da kwamitin sa ya kai jihar Barno.

Ya na magana ne sakamakon abubuwan da idon su da binciken da suka gudanar a Jihar Barno ya tabbatar musu cewa akwai hujjoji masu nuna wasu kungiyoyin agaji, wato NGOs a jihar na yi wa Boko Haram aiki.

“Mun je kuma cikin abubuwan da mu ka duba, har da zargin da ake yi wa wasu kungiyoyin bayar da agaji cewa su ka yi wa Boko Haram aikin ba u bayanai na sirri, ba su kayyaci da abinci da magunguna da sauran su.” Inji Ndume.

Ya ce a can baya ba ya son yin irin wannan maganar, amma yanzu da bayanai suka rika fitowa karra, ta fito fili cewa wata kungiya ko wasu kungiyoyin agaji biyu na taimakon Boko Haram.

Ndume ya ce amma za su yi bincike kuma za a ji abin da binciken zai fito da shi.

Ndume ya tunatar da cewa wasu kungiyoyin sun rika murnar sako ‘yan matan Chibok, saboda da su aka yi amfani wajen tattauna batun sako su.

Ndume ya yi wannan ikirari ne bayan sojoji sun zargi wasu kungiyoyin da taimakon Boko Haram.

Haka nan kuma Dan Majalisar Tarayya, Gudaji Kazaure, a cikin shekarar da ta gabata, ya yi zargin cewa wasu kungiyoyin agajin fa ‘yan ta’adda ne.

Daga nan kuma Ndume ya ragargaji yadda aka shirya tattauna sako dalibai kusan 100 musulmai, aka ki sakin Kirista guda daya.

“Idan da ni ne ake tsara yarjejeniyar da ni, idan suke saki dalibai musulmi 100 suka ki sakin Kirista daya, zan ce na yanke yarjejeniyar. Tunda dai gwamnati ce ke biyan kudin diyyar.”

“Idan ku ka ce min ga yara 100, amma mun rike guda daya, sai in ce duk ku hada duka ku rike.” Inji Ndume.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment