Pages

Friday 18 October 2019

An karrama Ali Nuhu a Indiya

An karama tauraron fina-finan Hausa Ali Nuhu a Indiya, kamar yadda ya bayyana wa BBC.

Wasu dalibai 'yan Arewacin Najeriya da ke karatu a kasar Indiya da malamansu Indiyawa ne suka gayyaci jarumin bikin Ranar Al'adu kuma suka karrama shi a wajen taron.






"Daliban na karanta fanni daban-daban kama daga fannin likita zuwa hada magunguna da injiniya da dai sauransu," in ji Ali Nuhu.


Jarumin ya ce baya ga wadannan dalibai, wasu makarantu a kasar sun ba shi lambobin yabo.

Ali Nuhu ya ce "akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba ni lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu."


Tauraron ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha'awar al'adun Hausawa.

"Wasu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe ta ke."

"Shi ya sa idan wani dan wasa ya zo taro irin wannan su kan karrama shi," in ji Ali Nuhu.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment