Pages

Thursday 17 October 2019

Ba za mu tafi yajin aiki ba>>Kungiyoyin kwadago

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun cimma matsaya da wakilan gwamnatin kasar kan karin albashin ma'aikata zuwa kashi 20 maimakon kashi 25 da kungiyoyin suka bukata ga ma'aikata da ke kan mataki na 7 zuwa 14.


Amma ba a cimma matsaya kan albashin ma'aikata da ke kan mataki na 15-16 ba.

An dai samu rabuwar kawuna tsakanin kungiyar NLC da TUC da ULC, sakamakon kafewa da wasu suka yi na babu ma'aikatu masu zaman kansu a batun karin albashin.

Kwamared Nasiru Kabiru sakataren tsare-tsare na kungiyar ULC ya shaidawa BBC jita-jita ce kawai ake yadawa amma babu batun tafiya yajin aiki alhalin su na tattaunawa da gwamnati wanda hakan ya sabawa dokokin kungiya.

"Mun cimma matsaya da gwamnati kan karin mafi kankantar albashin ma'aikata na Naira 30,000 a kowanne wata, kuma sun rattaba hannu kan za su biya ariyas saboda tun a watan Afirilu da ya wuce gwamnati ta rattaba hannu akan shi."

Sannan ya ce: "Za mu tabbatar da cewa an bai wa kowanne ma'aikaci wannan ariyas, haka nan wannan tsari har da matakin jihohi za a fara biya."

Ya kara da cewa, "Ko da ya ke a kwai wasu gwanonin jihohin da tuni suka fara biyan kananan ma'aikata albashinsu na naira 30,000, kuma duk jihar da ba ta bi wannan tsari ba kamar yadda muka sha nanatawa za mu dauki matakin da ya dace''.

Harwayau, Kwamared Nasir ya ce baya ga batun albashi, sun tattauna batutuwan walwalar ma'aikata da irin wahalar da ma'aikata musamman na banki ke sha.

Da kuma ma'aikatan kamfanin wutar lantarki wadanda sukan fukanci matsalolin wuta ta Ja su har a dangana da asarar rayuka, sai uwa uba batun rashin aiki da shi suka ce ya kamata gwamnati ta kara daukar ma'aikata.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment