Pages

Thursday 17 October 2019

Dan wasan baya na Liverpool Alexander Arnold ya shiga kundin tarihin Duniya saboda taimakon da ya bayar aka ci kwallo

Tauraron dan kwallon kasar Ingila me bugawa kungiyar Liverpool wasa, Trent Alexandra Arnold ya samu shiga kundin tarihin Duniya na 2020 a matsayin dan wasan baya daya fi bayar da taimako akan ci kwallaye a gasar Premierl League a kakar wasan 2018-19.




Arnold ya bayar da taimako aka ci kwallaye 12 a kakar wasan data gabata a Premier League inda a gaba dayan wasannin kuma ya bayar da taimako aka ci kwallaye 16.

Ya bayyana farin cikinshi da samun wannan kyauta inda yace a koda yaushe burinshi shine ya je gaba dan ya taimakawa kungiyarshibta ci kwallo, yace wannan kyauta ya sametane bisa aiki tare da abokan wasanshi da yayi.

Kuma abin alfaharice gareshi da iyalanshi.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment