Pages

Sunday 20 October 2019

Hukumar bada Lamuni ta Duniya ta goyi bayan Najeriya kan rufe iyakokinta

Hukumar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta goyi bayan Najeriya kan rufe iyakokinta da ta yi inda tace duk da rufe iyakokin na shafar kasashe makwafta amma dole kasuwancin da ake a iyakokin kasar ya kasance bisa doka da oda.




Daraktan kula da yankin Afrika na IMF, Abebe Salassie ne ya bayyanawa manema labarai haka a wajan taron da ake a tsakanin bankin Duniya da IMF din a babban birnin kasar Amurka, Washington DC.

Da yake amsa tambaya akan cewa ko kulle iyakokin Da Najeriya ta yi ya sabawa ka'idar alkawarin cinikin bai daya da kasar ta sakawa hannu?

Abebe yace kasuwanci tsakanin kasashen Afrika nada muhimmaci ba tare da shamaki ba amma kuma ya kamata ace ana yinshi bisa mutunta dokin kasa da kasa. Yace rufe iyakokin da Najeriyar ta yi duk da yana shafar kasashen Benin da Nijar amma matsalar fasa kwaurin kayane ya jawoshi kuma babu wanda zai so karfafa fasa kwaurin kayan.

Yace saidai saboda yanda rufe iyalar ke taba kasashen Nijar da Benin IMF zata so ganin an warware matsalar cikin sauri.

Yace idan rufe iyakokin ya dade to zai taba kasashen Nijar da Benin da suka dogara da Najeriya.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment