Pages

Sunday 20 October 2019

Gwamnan Jihar Oyo ya ziyarci wani masallaci inda ya bayyana cewa zai rusheshi

Gwamnan jihar Oyo,Seyi Makinde ya ziyarci wani masallacin juma'a a jihar inda ya bayyana musu shirin gwamnatinshi na rushe masallacin dan ya gina tashar motocin haya.



Gwamnan ya bayyana hakane ta shafinshi na Twitter inda yace ya ziyarci masallacin Juma'ar dake kan titin Iwo inda ya bayyana cewa gwamnatin shi na da shirin rushe masallacin da wata Coci da kuma wasu karin gine-gine dake yankin.

Saidai gwamnan ya basu tabbacin cewa gwamnatinshi zata bayar da isashshiyar diyya da zata isa a sake gina wani masallavin inda yace kuma wannan aiki bashi da nasaba da takurawa wani addini.

Ya kara da cewa gwamnatinshi na bukatar hadin kan jama'a akan wannan aiki.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment