Pages

Monday 21 October 2019

Iyaye na bada gudummuwa wajan lalatar da wasu malaman jami'a ke yi da dalibai mata dan basu maki>>Inji shugaban jami'ar ABU Zaria

Shugaban jami'ar Ahmadu Bello Zaria dake jihar Kaduna, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana cewa iyayen dalibai na taimakawa matsalar lalata da daliban dan bayar da maki da wasu gurbatattun malam jami'o'i ke yi.




Ya bayyana hakene a wata hira da aka yi dashi ta wayar salula a gidan rediyon Najeriya na Kaduna inda ya bayyana cewa tarbiyyace ta tabarbare.

Yace Jami'a ba kamar makarantar Sakandire bace. A jami'a ana baiwa dalibai yancin walwala saboda ana ganin sun fara mallakar hankalin kansu.

Yace amma matsalar da ake samu itace wasu iyayen tun a gida basa iya kwabawa 'ya'yansu idan sun yi ba daidai ba, asalima zaka ga wasu 'ya'yan sune ke juya iyayen.

Yace wasu iyayen da suka samu kudin banza kan rika baiwa 'ya'yansu kudin da suka wuce kima ta yanda zaka ga yarinya da kudi a asusun ajiyarta da nesa ba kusa ba ya nunka albashin malaminta, ga wayoyi masu tsada ga motoci masu tsada suna hawa.

To wannan ke sa sai kaga dalibi baya iya matar da hankali yayi karatu sai a fara bin gurbatattun malmai dan neman mafita.

Yace amma sun saka tsauraran matakai dan magance irin wanna matsalar.




Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment