Pages

Monday 21 October 2019

Yanda Mazan Kenya ke baiwa turawa masu yawon bude ido matansu na Aure su yi lalata dasu saboda tsananin talauci

Wani rahoto daga kasar Kenya ya bayar da labarin yanda wasu jama'ar kasar dake gabar Teku inda turawan kasashen yamma ke zuwa yawon bude ido ke baiwa turawan matansu suna kwanciya dasu saboda tsananin talauci.



Rahoton yace ba ma matan kadai ba, har mazan aure kan yi yarjejeniya da matansu cewa zasu je su yi lalata da matan turawan na wani lokaci kuma su yarda.

Wani dake zaune a yankin me suna James Kimani ya bayyana cewa tun shekarar 2018 yake baiwa turawa masu zuwa yawon bude ido matarshi su kwanta da ita saboda su samu kudin shiga.

Yace akwai baturen da yazo ya tambayeshi yana son ya samomai mace da zai kasance tare da ita kamij ya koma kasarshi, sai ya gayamai cewa akwai wata kanwarshi da zai kawomai tana da kyau da duk abinda ake bukata a tattare da mace, sai yaje ya kawomai matar tashi.

Yace kuma idan ta gama zama da baturen tana dawowa gida su ci gaba da rayuwar aure kuma suna son junansu har yanzu, ya kara da cewa itace ke rike da gidan.

Da aka tuntubi hukumar 'yansanda ta yankin, ta tabbatar da cewa wannan abu ya dade yana faruwa, hukumar 'yansandan tace akwai matan dake da maza biyu, Bature da baki dan Kenya.

Idan baturen ya zo gari sai ta koma zama dashi idan kuma ya tafi saita koma zama da dan kenya.

Hakanan an samu rahotannin yin lalata da kananan yara musamman mata wanda hakan ke kawo cikin shege da ba'a shirya mai ba da kuma yaduwar cututtukan da ake dauka wajan Jima'ai, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment