Pages

Sunday 20 October 2019

Liverpool ta buga kunnen doki da Man United bayan jera wasanni 17 tana nasara

A karin farko cikin wasanni 17 data jera tana yin nasara a gasar Premier League, Liverpool ta buga kunnen doki da Manchester United inda suka tashi 1-1 a wasan da suka buga yau.




Marcus Rashford ne ya fara ciwa Man United kwallo kamin aje hutun rabin Lokaci inda kwallon da saida alkalin wasa ya duba VAR kamin aka tabbatar da ita.

Sadio Mane ya ci kwallo saidai VAR din ta kashe ta.

Adam Lallana ne ya ceto Liverpool daga yin rashin nasara inda ya ci mata kwallo ana gaf da za'a tashi.

Andrew Robertson ya kamo Alexander Anold wajan yawan bada taimako aci kwallaye a matsayin dan baya inda shima a yanzu yake da guda 14.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment