Pages

Monday 21 October 2019

Matasa Sun Gudanar Da Zanga-zangar Rashin Kyawun Hanyar Suleja Zuwa Minna

Yanzu yanzu dubun dubatar matasa sun rufe babban titin Minna zuwa Suleja dake Jihar Neja, inda suke gudanar da zanga zangar lumana akan matsalar lalacewar hanyoyi da Jihar ke fama dashi.


Matasan na dauke da alluna da kwalaye wanda ke kira ga gwamnatin tarayya akan ta kawo wa Jihar dauki dangane da matsalolin hanyoyi da kusan dukkan titinun Jihar ke fama dashi, wadanda suke ganin gwamnatin Jihar ta kasa katabus akan matsalolin.


Jihar Neja dai itace Jihar dake da manyan tituna na gwamnatin tarayya fiye da kowace Jiha a Nigeria kuma itace Jihar da ta hada sauran Jihohin Arewa dana kuduncin kasar nan, Saidai kusan dukkan hanyoyin ta a lalace suke baya ga titin Kontagora zuwa Yauri, da aka kammala da titin Kontagora zuwa Makera da New Bussa zuwa Kaiama da akeyi a halin yanzu da kuma titin Kontagora zuwa Bangi da gwamnatin tarayya ta amince da aikin sa dake yankin Neja ta Arewa wadanda Sanata Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) ya gabatar da koken yin su.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment