Pages

Sunday 20 October 2019

Ronaldo ya fi samun kudi a Instagram fiye da Albashin da Juventus ke biyanshi

Wani bincike da aka yi ya tabbatar da cewa tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa Juventus wasa ya fi samun kudi da shafinshi na Instagram fiye da albashin da kungiyar da yake bugawa Kwallo,Juventus ke biyanshi a shekara.




Wannan bincike wani kamfanin kula da shafukan sadarwar zamani me suna Hopper HQ ne yayi kamar yanda Buzz Bingo suka ruwaito. Ronaldo ya samu Miliyan 47.8 a tallace-tallacen da yawa kamfanoni a shafinshi na Instagram, a yayin da albashinshi da Juventus ke biyanshi a shekara miliyan 34 ne kamar yanda Goal ta ruwaito.

Ronaldo ne mutumin da ya fi yawan mabiya a shafin na Instagram inda yake da mabiya miliyan 186 wanda hakan yasa kamfanoni ke biyanshi makudan kudade dan ya saka musu talla a shafin nashi.

Ana biyan Ronaldo dala 975,000 akan duk talla daya da zai saka a shafin nashi wannan yasa ya zarta shahararrun masu amfani da shafin wajan samun kudi irin su Kylie Jenner,Selena Gomez, Lionel Messi, Emily Ratajkowski.

Babban abokin takarar Ronaldo a kwallo,Lionel Messi na samun kasa da rabin kudin da Ronaldon ke samu a shekara daga shafin na Instagram inda yake samun Miliyan 23.3.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment