Pages

Friday 18 October 2019

Sauya Min Maganata Ta Aka Yi Cewa Na Ce Bayan Allah Ba Ni Da Wanda Ya Wuce Jonathan>>Gwamnan Bauchi,Bala Mohammed

Yayin da yake magana a madadin gwamnan, kwamishinan yada labarai na jihar Bauchi, Ladan Salihu ya kara da cewa a koda yaushe Gwamna Sanata Bala Mohammed yana martaba addininsa, kawai wasu abokan hamayyar siyasa ne suka sauya maganar. Kawai shi dai ya ce ne ba shi da ubangidan da ya wuce Jonathan a siyasa.


A 'yan kwanakin nan ne dai aka yi ta yada wani bidiyo, inda aka nuno gwamnan Bauchi yana cewa bayan Allah ba shi da wanda ya wuce Jonathan.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment