Pages

Sunday 20 October 2019

Shugaba Buhari zaikai ziyara kasar Rasha gobe Litinin

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Rasha ifan Allah ya kaimu gobe inda zai halarci taron hadin kan kasashen Afrika da Rasha da ciyar da nahiyar gaba.




Shugaba Buhari a lokacin ziyarar tashi zai gana da shugaba Vladmir Putin na Rasha dan tattaunawa kan yanda Najeriya zata amfana da dabarar da Rasha ke amfani da ita wajan fitar da Gas zuwa kasashen waje.

Sauran abubuwan da za'a tattauna a wajan taron sun hada da ci gaban kimiyya da fasa da kasuwanci da tsaro da dadai sauransu tsakanin Afrika da Rasha.

Wadanda zasu wa shugaban rakiya zuwa Rasha sun hada da gwamnonin Jihohin Jigawa, Gombe da Ekiti da Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama da na kasuwanci da karamin ministan Mai dadai sauransu kamar yanda Me magana yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya sanar.



Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment