Pages

Sunday 20 October 2019

'Yan gidan yarin kasar Amurka sun fi ma'aikatan Najeriya samun kudi>>Inji Ministan Cikin gida

Ministan harkokin cikin gida kum, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana cewa kudin da ake kula da 'yan gidan yari a kasar Amurka ya fi mafi karancin albashin da ake biyan ma'aikata ko kuma ake kokarin fara biyan ma'aikata a Najeriya na Naira dubu 30.



Aregbesola ya bayyana hakane a wajan bayani da yake bayarwa gaban 'yan majalisar tarayya kan yadda ma'aikatarshi zata kashe kudi a shekarar 2020.

Ya bayyana cewa 'yan gidan yarin kasar Amurka ana kula dasu akan kwatankwacin kudin Najeriya Naira dubu 31 a kullun yayin da 'yan Gidan Yarin Najeriya kuwa ana kula dasune akan Naira 730 a kullun, kamar yanda NewTelegraph ta ruwaito.

Yace a wasu jihohin na kasar Amurka ma kudin da ake kula da 'yan gidan yari yana kai Naira dubu 60. Ya kara da cewa duk da dai tattalin arzikin Najeriya be kai na kasar Amurka ba amma kudin da ake kula da 'yan gida yarin kasar ya fi wanda ake kula da 'yan Gidan Yarin Najeriya sannan kuma ya fi kudin da ake biyan ma'aikata a matsayin mafi karancin albashi na dubu 30.



Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment