Pages

Saturday 7 December 2019

Everton ta huce haushin cin da Liverpool ta maka akan Chelsea da ci 3-1

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sha kashi da ci 3-1 a hannun fusatattun Everton da suka huce haushin cin Liverpool ta musu 5-2 a wasan da suka buga a makon da ya gabata.



Ga dukkan alamu korar da Everton ta wa kocinta za'a iya cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu dan kuwa gashi wasanta na farko bayan korar tashi ta yi nasara.

Kovavic ne ya farkewa Chelsea kwallo 1 cikin kwallaye 3 da aka zurara mata yau, kuma ya taka rawar gani sosai a wasan na yau.

Richarlison ne ya ciwa Everton kwallo daya yayinda Dominic ya ci mata kwallaye 2 wanda sune kwallaye na farko da ya taba ci a wasa 92 daya buga.

Kocin Everton Duncan yayi wata itin murna yayin da suka ci kwallo ta 2 data dauki hankula.




Kwallo ta 3 da aka ci Chelsea, golanta Kepa ne yayi kuskure inda ya baiwa dan wasan Everton wanda kuma ta shiga raga.








Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment